ABNA24 : Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa an kai harin ne a kan wani asbiti wanda ake kira Asshifa a jiya Asabar
Wasu kafafen yada labarai na Turkiyya sun tabbatar da cewa mayakan kungiyar YPK masu samun goyon bayan Amurka ne suka kai harin.
Tun shekara ta 2016 yankunan kasar Siriya wadanda suke kan iyakar kasar da kasar Turkiya suna fama da tashe tashen hankula, saboda samuwar sojojin Amurka da na turkiya a cikinsu da kuma kungiyar yan ta’adda ta kurdawa masu sun ballewa daga kasar ta Siriya.
342/